Headlines
Loading...
Ingila ta dauki mataki kan wariyar launin fata a Rasha - Young

Ingila ta dauki mataki kan wariyar launin fata a Rasha - Young

Dan wasan Ingila da kuma Manchester United, Ashley Young ya ce sun tattauna matakin da ya dace su dauka idan sun fuskanci wariyar launin fata a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Bai dade ba da aka ci tarar hukumar kwallon kafa ta Rasha kudi fan dubu 22, kan wariyar launin fata. An ti tarar kasar ne bayan da wasu 'yan kallo suka furta kalaman wariya ga 'yan wasan Faransa a karawar sada zumunci a da suka yi a watan Maris. '

'Idan mutum yana fili ban san yadda zai ji ba idan aka nuna masa wariya' in ji Young mai shekara 32.
Ya ce 'amma mun tattauna a kan matakin da ya kamata mu dauka da abin da ya kamata mu kauracewa.' Ya kara da cewa 'suna fatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, za ta yi maganin matsalar.'


'Yan wasan Faransa da suka hada da Paul Pogba, da Ousmane Dembele, da kuma Ngolo Kante ne aka ruwaito ana furta wa kalaman nuna wariya a wasan sada zumunci da suka doke Rasha da ci 3-1.
An buga wasan ne a filin wasa na Krestovsky da ke birnin St Petersburg, kuma filin na daga cikin wadanda za a buga gasar cin kofin duniya.

0 Comments: