
'Yan sandan Merseyside sun ce suna
sane da sakonnin barazanar kisa da ake aike wa golan Liverpool Loris
Karius bayan wasan karshe na gasar zakarun Turai.
Karius ya barke da kuka bayan an tashi daga wasan sannan kuma ya nemi afuwar magoya baya.
"Muna daukar irin wadannan sakonnin da ake wallafa wa a shafukan zada zumunta da muhimmanci. Za mu yi binciken kan dukkan laifukan da aka aikata," a cewar 'yan sanda.
"Jami'ai na sane da sakonnin barazana da aka tura ta shafukan sada zumunta.
"Muna tunatar da masu amfani da wadannan shafuka cewa za a binciki duk wata al'amari da halayya mai kama da wannan."
Dan wasan ne ya bai wa Karim Benzema kwallon farko da ya ci cikin sauki.
Daga bisani Karius ya kasa tare kwallon da Gareth Bale ya buga daga nesa wacce ta bai wa Madrid damar saka kwallo ta uku da kuma lashe kofin.
0 Comments: