Gareth Bale, wanda shi ne ya taimaka
wa Real Madrid ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai, ya ce bai gamsu da
yadda kociyan Madrid din Zinadine Zidane, ke kin sanya shi a wasa yadda
ya kamata ba.
Ina so na rinka yin wasa a kowanne mako, amma ban samu hakan ba a nan, a kan wani dalili da ban tabbatar ba, in ji Bale Ya kara da cewa idan bai samu damar buga wasanni sosai a Real Madrid din ba, to zai zauna ya yi tunanin makomarsa.
Bale ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai sau hudu zuwa yanzu a zaman sa a kungiyar ta Real Madrid da ke kasar Spaniya.
Akwai yi wuwar cewa kungiyoyi da dama za su iya yin zawarcinsa idan ya nuna aniyar barin kungiyar tasa.
A baya dai kungiyar Manchester United ta taba nuna sha'awarta kan zawarcin dan wasan. Sai
dai ba kowacce kungiya ce za ta iya biyan sa kudin da Real Madrid ke ba
shi ba, domin ana ganin cewa Bale, na daukar albashi da ya kai Fan dubu
400, bayan an cire haraji a kowanne mako. A sheakarar 2013, ne Real Madrid ta sayi Bale daga Tottenham a kan zunzurutun kudi fan miliyan 86.
Bale yana da kwantiragi da Real Madrid wadda za ta kare a shekara ta 2022.
0 Comments: