Headlines
Loading...
Babu Gwamnan da ya kula da Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna kamar El-Rufa’i – Farfesa Chom

Babu Gwamnan da ya kula da Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna kamar El-Rufa’i – Farfesa Chom

Shugaban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Farfesa Emmanuel Joseph Chom ya mayar da martani ga masu cewa babu wani abin a zo a gani da gwamnatin jihar ta yi wa kwalejin saboda mazauninta yana Kudancin Jihar ne, inda ya ce babu gwamnatin da ta taba kashe wa makarantar kudi kamar yadda Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ya yi.

Farfesa Emmanuel Chom ya ce Gwamna El-Rufa’i ya kashe wa kwalejin zunzurutun kudi Naira biliyan daya da miliyan 200 wajen gyare-gyaren da suka shafi ta da sababbin gine-gine da gyara ajujuwa da dakunan kwanan dalibai da kuma katange makarantar.
Farfesa Emmanuel Chom ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai ciki har da Aminiya a ofishinsa da ke matsugunin makarantar na dindindin da ke Gidan Waya a karamar Hukumar Jama’a.


Farfesa Chom, ya ce wannan wani dauki ne da gwamnatin jihar ta yunkuro don tallafawa inda bayan kwashe shekara 21 da tantance kwasa-kwasan da suke koyarwa a makarantar, ba a sake waiwayarsu sai yanzu da Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta kasa (NCCE) ta tantance kwasa-kwasai 20 cikin 29 da suke koyarwa, “Wannan duk kokari ne da Gwamnan Jihar ke yi na mayar da kwalejin daya dage cikin kwalejojin ilimi mafiya inganci a duniya,” inji shi


Farfesa Chom ya ce ta bangaren inganta koyarwa da sauran ma’aikata, gwamnatin jihar tana da burin nan gaba kadan za a samar da masu digirin digirgir akalla biyu a kowane sashi, wanda a kan haka har Asusun Kula da Manyan Makarantu (TetFund) ya dau nauyin malamai fiye da 200 domin karo ilimi kuma zuwa yanzu mutum 30 daga ciki sun kammala digirin digirgir daga cikinsu.

0 Comments: