Headlines
Loading...
Manoman Najeriya Suna Fama Da Tsadar Abinci

Manoman Najeriya Suna Fama Da Tsadar Abinci

Kwararru sun bayyana matakai da za’a iya bi wajen shawo kan matsalar karancin abinci da kuncin rayuwa da al’ummar Najeriya ke ta korafi a kai tare da danganta lamarin da iftila’i na ambaliyar ruwan sama da aka yi ta samu cikin wannan shekara ta 2020.


Karin farashin man fetur na daya daga cikin abubuwa da suke kara kuncin rayuwa a kan al’ummar Najeriya, haka zalika batun wutan lantarki ke ci gaba da karfen kafa ga sana’o’I manya da kanana a Najeriya.

Sakataren yada labarai na kungiyar manoma a Najeriya Afan Muhammad Magaji,ya ce abin dake kawo karancin abinci shine wasu na sayen abincin suna adanawa, lamarin da ka iya sa farashin abinci ya yi tashin goron zabi.

A cikin wani rahoto da Babban Bankin duniya ya fitar, an gano faduwar da aka samu a farashin man fetur da kuma annobar COVID-19 ta sa Najeriya cikin matsalar tabarbarewar tattalin arziki wanda a cewar rahoton idan ba’a gaggauta samo mafita da ka iya kawo sauyi ba, kasar za ta dade cikin wannan yanayi.

‘Yan Najeriya da dama ne suka yi ta tofa albarkacin bakinsu game da kuncin rayuwa musamman a wannan yanayi da a ka yi kari a farashin man fetur da na wutar lantarki a kasar.

A sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa wannan matsalar da Najeriya take ciki ta shafi duniya baki ɗaya kuma gwamnatin Buhari ta fara bin matakai don shawo kan matsalar.

Hanyoyin shawo kan wannan matsala, shugaba Muhammadu Buhari ya dauka sun hada da umarnin da ya bayar na fitar da abinci kusan ton 30,000 na masara ga masu samar da abincin dabbobi domin sauƙake farashi, ya kuma baiwa manoman kasar shawara da su kara kaimi wajen noma abinci a kasar duba da cewar kasar bata da kudin da biya wajen shigowa da abinci daga wasu kasashen

0 Comments: