Headlines
Loading...
Da ma matan 'yan China na aurar bakar-fata?

Da ma matan 'yan China na aurar bakar-fata?

Xu Jing, ta ce sun fara soyayya, to amma da farko sun sha wuya.
Sun hadu ne a wani kebantaccen waje a wani otel na Fairmont da ke Nairobi.
Xu ta ce ' Iyayena ba su san Afirka sosai ba. Ba su taba zuwa Kenya ba, don haka suka kasance cikin damuwa.'
Masoyan biyu sun fara soyayya ne bayan da aka tura Henry zuwa China domin ya koyo yaren Mandarin a wani bangare na sabon aikin da ya samu.
Ya kwashe tsawon lokaci yana koyon yaren, kafin daga bisani suka hadu da mahaifin Jing bayan ya je wajen su inda suka ba shi abinci, sannan kuma ya nemi ya sa masa albarka a kan abin da ya kawo shi kasar.
Henry ya ce "Mahaifin Jing bai ce komai ba, sai na shiga damuwa a kan abinda ya ke tunani, shin ko ya ji dadin abincin da muka bashi?"
Bayan shekara 10, Henry ya kware a yaren Mandarin, daga baya sai ma'auratan suka koma Nairobi, babban birnin kasar Kenya da zama, inda kuma suka haifi yara biyu.
Yanzu haka Jing tana koyar da yaren Mandarin a wata jami'a a Nairobi.
Jita-jita
Labarin Jing da Henry ya samu nasara, to amma dangantakar da ke tsakanin 'yan kasar China da ke Kenya tana tangal-tangal.



A kan hanyar Thika, wani kamfanin kasar China ya gina wata babbar hanya da ta hada zuwa Nairobi daga garin na Thika, inda ake kiran wajen Thika babies.
A cewar wasu ma su tsegumi, ma'aikatan da ake aiki a kamfanin gine-gine na kasar 'yan China sun yi wa da yawa daga cikin matan da ke zaune a wajen ciki kafin su bar wajen.
Kafafen yada labarai sun rawaito labarin wata yarinya 'yar makaranta da wani ma'aikaci dan kasar China ya yi wa ciki wadda kuma ta kasa gane shi a cikin daruruwan ma'aikatan kamfanin gine-ginen da ke Thika.
Haka dai ake ta yada jita-jitar cewa 'yan kasar Chinan da ke aikin ginin hanya a yankin Thika, suna yi wa mata ciki, abin da ba za a iya tantancewa ba.
Wani wanda ya ke fassara yaren China a Kenya, wato Thatcher da ake zaune a kusa da hanyar Thika, ya ce yana ganin nan da shekara 15 zuwa 20, idan yaran da aka haifa da ake zargin 'yan kasar Chinan ne suka yi cikinsu suka girma har suka je makaranta, za a gano gaskiyar lamarin.
Yadda yanayi ke canzawa a Afirka
Bacewar iyaye maza ba ita ce matsala ba a yawancin gidajen Kenyan da 'yan kasar China suka yi wa wata ciki.
To amma ga Jing, wadda ta girma a lokacin da ake da dokar haifar da daya a China, ta ce wani lokaci tsabagen yawan dangi kan zama babban lamari.

Henry ya ce 'Mu mun saba da tara iyalai, ko kuma kaga gida akwai iyalai da yawa, wani lokaci ko da gidanka kai kadai ne sai matarka da yaranka, 'yan uwanka kan zo su zauna da kai, wani lokaci su jima a wajenka.'
Ya ce to amma 'A China, ba su da wannan al'ada ko dabi'a. saboda ba su da yawan iyalai, su a kasarsu, 'yan uwanka kan zo wajenka su zauna da kai ne na dan gajeren lokaci.'
Irin wadannan al'adu, shi ya banbamta mu da su, haka akwai kuma wasu al'adunma da suka banbamta mu da dama, inji Henry.
A kasar Kenya, mutane na daukar komai cikin sauki, domin suna more rayuwarsu, ba kamar a kasar China ba.
'Yan kasar China na zuwa Kenya tare da cimma abin da suke so, suna aiki na tsawon sa'oi, sukan dauki lokacin hutu kadan, sannan sukan yi aiki ba dare ba rana domin su tabbatar da sun kammala komai cikin sauki.
Abin da Jing da Henry suka fahimta ke nan a tsakaninsu.
Jami'ar da Jing ke aiki wato The Confucius Institute, na daya daga cikin makarantun da gwamnatin China ke daukar nauyi, kuma ta yi hakan ne domin ta kara karfafa dangantaka tsakaninsu da China.



Yawancin iyaye mata a Nairobi na son magana da Xu da kuma 'ya'yanta idan sun ganta, idan an ganta akan ce ga uwa 'yar China.
Henry ya ce 'Yaranmu na kama da 'yan kasar Kenya, a saboda haka idan na fita tare da su, mutane kan tambaye ni wane yare suke yi?'.
'Idan na ce mu su Chinese, su kance me? Abin ya kan burge mutane har sukan so su rinka yin mana tambayoyi, wani sa'in ma sukan zama abokanmu' inji Henry.
A nata bangaren kuwa wato Jing, cewa ta yi ' Na kan yi kewar kasata ta asali wato China, amma Kenya yanzu ita ce gidana.'

0 Comments: